Kamfanin dillancin labarai na kasar Masar MENA, ya bayyana cewar, tun bayan da kasar Isra'ila ta fara kai hari a zirin gaza a ranar 8 ga watan Yuli, wannan shi ne karo na ukku, da kasar Masar, a matsayin ta na mai shiga tsakani, ta kara kaimin tatttaunawar da take yi tsakanin bangarorin Isra'ila da na kungiyar Hamas.
Harin baya-bayan nan, da Isra'ila ta kai a kan zirin Gaza, ya yi sanadiyyar mutuwar Palasdinawa fiye da dubu 1,950 kuma wasu Palasdinawa kimanin 10,200 sun sami rauni, a kuma bangaren Isra'ila hare-haren Hamas sun haifar da mutuwar sojojin Isra'ila 64 da kuma farar hula 3.
Kawo ya zuwa yanzu Isra'ila ta ki amincewa da yawancin sharuddan da Palasdinawa suka gabatar domin samar da tsagaita wuta na din-din, sharuddan da Palasdinawa suka gabatar sun hada da bukatar dage takunkumin shekaru 7, da Isra'ila ta kakabawa zirin Gaza, da kuma bude kan iyakokin Palasdinawa tare da sallamar fursunoni Palasdinwa, wanda aka amince da shi da Isra'ila a wani shiri da ake yi, a baya, na musayar firsunoni tsakanin Isra'ila da Palasdinu.
Hakazalika Palasdinawan suna bukatar Isra'ila ta ba su damar gina tashar jiragen ruwa da kuma gina filin jirgin sama a Gaza, tare da ba su damar gudanar da wani babban taro na samun kudadde na guddumuwa daga kasashen duniya domin sake gina zirin Gaza. (Suwaiba)