Bisa kididdigar da Palesdinu ta yi, an ce, mutane a kalla 1422 ne suka mutu a sakamakon aikin soja da Isra'ila ta dauka a zirin Gaza, kana mutane fiye da 7800 sun ji rauni, kuma yawancinsu fararen hula ne. Yawan mutanen da suka mutu ko raunata ya karu sosai a sakamakon ruwan boma-bomai da sojojin Isra'ila suka yi a kwanakin baya.
Kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da taro cikin gaggawa game da hali mai tsanani a zirin Gaza da aka kai hare-hare ga sansanin 'yan gudun hijira na MDD dake zirin Gaza, inda mataimakiyar babban sakatare mai kula da harkokin jin kai na MDD Valerie Amos ta yi bayani cewa, yanzu babu inda ake da zaman lafiya a zirin Gaza.
Hakazalika kuma Amos ta bayyana cewa, a halin yanzu mutane fiye da dubu 440 sun rasa gidajensu, wanda ya kai kashi 24 cikin dari na yawan mutane a zirin Gaza. Mutane dubu 240 a cikinsu sun zabi kaura zuwa sansanin 'yan gudun hijira na MDD dake dab da sashen bada taimako ga 'yan gudun hijira a gabashin Palesdinu. (Zainab)