Ma'aikatar kiwon lafiya ta Falesdinu ta sanar da cewa, galibin mutanen da suka rasu fararen hula ne ciki har da mata da yara da dama.
A jawabin da firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi yayin taron kwamitin kula da harkokin diplomasiyya da tsaron kasa da ke majalisar dokokin kasar ta Isra'ila, da aka gudanar a ran 10 ga wata, ya ce, a halin yanzu, kasar ba ta da wani shirin kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas.
A wannan rana kuma, shugaban Felesdinu Mahmoud Abbas ya yi shawarwari da ministan harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ta wayar tarho, inda ya yi fatan cewa, bangarorin biyu za su yi kokari tare, domin tsagaita bude wuta a yankin Gaza cikin hanzari.
A wani ci gaban kuma, shi ma shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi shawarwari tare da firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ta wayar tarho, inda ya jaddada cewa, tilas ne kasar Isra'ila ta dakatar da hare-haren da ta kai ba tare da bata lokaci ba.
Bugu da kari, shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya yi kira ga Isra'ila da Falesdinu da su kai zuciya nesa, kana su fara yin shawarwari a tsakaninsu. (Maryam)