Babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya bayyana farin cikinsa game da cimma yarjejeniyar tsawaita dakatar da bude wuta a Gaza, yana mai fatan hakan zai bada damar kaiwa ga cimma yarjejeniya mai dorewa.
Mr.Ban wanda ya bayyana hakan, biyowa bayan amincewar da bangarorin Isra'ila da Falasdinu suka yi, da shawarar dakatar da bude wuta har tsahon sa'o'i 72 sakamakon shiga tsakani da Masar ta yi, ya kuma kara da kira ga dukkanin bangarorin da wannan lamari ya shafa, da su ci gaba da shawarwari da juna, domin kaiwa ga lalubo hanyar kawo karshen rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa.
Daga nan sai ya alkawarta goyon bayan MDD, da tallafi ga duk wata manufa ta aiwatar da sulhu, da wanzar da zaman lafiya a yankin na Gaza.