Mr Ban ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya bayar ta hannun kakakinsa,inda ya yi allahwadai da kisan na Gaza da kuma bam din da aka dana cikin wata motar Bas a kusa da birnin Tel Aviv ranar Lahadi.
Babban sakataren na MDD ya kuma yi amfani da wannan dama wajen mika ta'aziyarsa ga iyalan wadanda hare-haren suka shafa. Kafofin watsa labarai na bayyana cewa,hare-haren sun zo ne bayan da wasu maharan Palasdinawa suka harbe wasu 'yan Isra'ila har lahira yayin da suke kokarin gyara shingen tsaro.(Ibrahim)