in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hamas ta kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da Isra'ila
2014-07-05 16:21:34 cri
Wani jami'in kungiyar Hamas dake mallakar yankin Gaza ya bayyana a ran 4 ga wata cewa, dukkanin bangarorin biyu na Hamas da Isra'ila ba su fatan ganin ci gaban ricikin dake tsakaninsu a yankin Gaza, shi ya sa, bisa taimakon da jami'an kasar Masar da MDD suka bayar, kungiyar Hamas ta kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da Isra'ila a wannan rana.

Kana, bisa labarin da aka samu daga kafofin watsa labaran kasar Isra'ila, an ce, yayin da ministan harkokin wajen kasar Avigdor Lieberman ya yi tsokaci kan wannan yarjejeniya, ya nuna cewa, bai amince da wannan yarjejeniya ba, a cewarsa wannan wani babban kuskure da gwamnatin kasar Isra'ila ta yi, sabo da dakarun Falesdinu dake yankin Gaza ba su taba dakatar da nazarin binciken roka mai cin dogon zango ba, kuma suna ci gaba da kai hare hare kan Isra'ila. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China