Mayakan Izz el-Deenal-Qassam dake matsayin reshin soji na kungiyar Hamas mai iko da zirin Gaza, sun bayyana rashin amincewa da sabon matakin dakatar da bude wuta, wanda aka shawarta aiwatarwa bisa dalilai na jin kai a Larabar nan.
Hakan dai na zuwa ne bayan da kungiyar 'yantar da Palasdinawa ta PLO ta bayyana amincewa da hakan, tana mai cewa bangarori daban daban ciki hadda Hamas da Jihad na Palasdinu, sun cimma matsaya guda game da wannan batu, tare da aniyar sa kaimi ga tabbatar da hana ci gaba da musayar wuta har tsawon sa'o'i 72 bisa shawarar MDD.
Sai dai a daya hannun Izz el-Deenal-Qassam ta fidda wata sanarwa ta kafar talabijin, tana mai cewa idan har ana burin aiwatar da wannan shawara, to ya zama dole sojin Isra'ila su dakatar da kai hare-hare, da kuma janye dukkan shingen da aka kafa a yankunan Gaza har na tsawon shekaru 7. Kaza lika dakarun rundunar sun nanata wajibcin baiwa Palasdinawa tsaro, da mutunta mutuncinsu da 'yancin kansu.
Ya zuwa yanzu dai an shiga mako na uku ke nan da fara musayar wuta tsakanin tsagin Palasdinu da na Isra'ila, kuma ko da yake a baya an kai ga tsagaita wuta a wasu 'yan lokuta, sai dai rikicin ya kara tsananta tun daga ranar Talata.
An ce Palasdinawa a kalla 120 ne suka rasa rayukansu, sakamakon hare-haren da sojin Isra'ila suka kaddamar a baya bayan nan, lamarin da ya sanya adadin asarar rayukan Palasdinawan kaiwa ga mutum 1231, yayin da wasu fiye da 7000 suka samu raunuka, wadanda kuma kashi 80 bisa darin su fararen hula ne.
A nata bangare kuwa, Isra'ila ta rasa sojinta 53, tun fara wannan fada a ranar 17 ga watan nan. (Amina)