in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hamas da Isra'ila sun amince da tsagaita wuta na awo'i 12
2014-07-26 16:36:28 cri
Bisa shawarar MDD da sauran bangarori, Palasdinu da Isra'ila sun amince da dakatar da bude wuta tsakaninsu a daren jiya ran 25 ga wata. A wannan rana, kungiyar Hamas ta bayyana karbar shawarar da MDD ta yi mata na tsagaita bude wuta a zirin Gaza na awo'i 12 bisa dalilin jin kai.

Kakakin kungiyar Hamas Sami Abu-Zuhri ya bayar da wata sanarwar a wannan rana cewa, darikoki daban-daban na Palasdinu ciki hadda Hamas sun tsai da matsaya daya na amincewa da shawarar MDD, na a dakatar da musayar wuta daga karfe 8 na safen ran 26 ga wata zuwa karfe 8 na daren wannan rana. Bisa labarin da kafar yada labaru ta Isra'ila ta bayar, an ce, Benjamin Netanyahu, firaministan Isra'ila ya amince da daina kai hare hare daga karfe 7 na safen wannan rana da muke ciki kan zirin Gaza.

Ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry da takwaransa na kasar Amurka John Kerry, babban magatakardan MDD Ban Ki-Moom da takwaransa na kungiyar kawancen kasashen Larabawa AL Nabil el-Araby sun kira wani taron manema labaru na hadin gwiwa a daren ran 25 ga wata a birnin Alkahira, domin yin kira ga Palasdinu da Isra'ila da su amince da sabbin shawarwarin tsagaita bude wuta a kalla kwanaki 7, bisa dalilin jin kai da albarkacin bikin karamar salla.

A nata bangare kuma, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya yi tir da harin da aka kaiwa wata makaranta a ran 25 ga wata a arewacin Gaza, tare kuma da kalubalantar bangarorin biyu da su amsa kiran kasashen duniya, har ma da tabbatar da dakatar da jin karar makamai nan da nan, domin kaucewar tsanantar da halin da ake ciki da asarar fararen hula. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China