in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake yin rikici tsakanin Palestinu da Isra'ila
2014-08-08 20:45:11 cri
A safiyar ranar Jumma'a 8 ga wata da misalin karfe 8 bisa agogon wurin, aka kawo karshen awoyi 72 na tsagaita bude wuta tsakanin dakarun Palestinu a Gaza da dakarun Isra'ila, a don haka, kungiyar dakarun Gaza ta sake harba roka zuwa Isra'ila. Ya zuwa karfe 11 na safiyar yau, Isra'ila ta kai hari ta jirgin sama kan yankin Gaza, har ma jami'an Isra'ila masu tsattsauran ra'ayi sun yi barazanar dawo da tawagar kasar dake yin shawarwari a Masar.

Kafin wannan, Masar ta tattauna game daba da shawarar kara wa'adin tsagaita bude wuta zuwa awoyi 120. Game da wannan batu, Isra'ila ta nuna amincewa, yayin da kungiyar Hamas ta bayyana cewa, za ta ci gaba da kai hari idan Isra'ila ba za ta kawar da shinge da ta dasa ajanye sojojinta wadanda ke yi ma yankin Gaza kawanya ba. Bayan kawo karshen wa'adin tsagaita bude wuta a yau kuma, ya zuwa karfe 10 da minti 30 na safiyar yau, an harba roka kimanin 20 daga yankin Gaza zuwa Isra'ila. Daga bisani, kungiyar PIJ ta sanar da daukar alhakin lamarin. Abin da ya sanya Isra'ila ta yi ramuwar gayya da hare-haren jiragen saman yaki daga bisani.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China