Sabbin hare-haren da Isra'ilan ta kaddamar dai sun hallaka Palesdinawa 10 tare da jikkata wasu kimanin 40, ciki hadda kananan yara da dama.
Da yake tsokaci game da hakan, firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce ya zama wajibi kasarsa ta shirya ci gaba da kaddamar da hare-hare na tsahon lokaci, har sai ta lalata dukkanin hanyoyin karkashin kasa, da mayakan Palasdinawa ke amfani da su wajen kai mata farmaki.
A daya bangaren kuma babban sakataren MDD Ban Ki-moon, ya yi kira ga Palesdinu da Isra'ila, da su tsagaita bude wuta domin kare alfarmar ranar karamar salla ba tare da gindaya wani sharadi ba, kana ya bukace su da tsagaita bude wuta cikin dogon lokaci, domin aza tubalin gudanar da shawarwari a tsakaninsu.
Bisa kididdigar da hukumar kiwon lafiya ta Palesdinu ta yi, an ce, matakan soja da dakarun Isra'ila suka dauka tun daga ranar 8 ga watan nan, sun haddasa mutuwar Palesdinawa fiye da dubu daya, kana wasu mutanen fiye da dubu 6 da yawancinsu fararen hula ne sun jikkata.
A bangaren Isra'ila kuwa, an ce sojojin kasar ta 42 ne, da kuma wasu fararen hular kasar suka rasa rayukansu a sakamakon wannan dauki ba dadi. (Zainab)