Kasar Isra'ila ta amince da tsagaita wuta na awoyi 72, a sakamakon shiga tsakani na kasar Masar, tsagaita wuta za ta fara aiki daga yau ranar Litinin, kamar dai yadda wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
A can baya Isra'ila da kungiyar Hamas sun dakatar fadar ta awoyi 72, tun daga ranar Talatar zuwa Juma'ar da ta wuce, to amma kuma kokarin da aka yi na samar da wata yarjejeniya tsagaita wuta mai dorewa, ya ci tura a yayin da kungiyar Hamas ta ci gaba da jefa rokoki a kudancin Isra'ila a safiyar Juma'a, daga nan kuma sai Isra'ila ta mai da martini da kai hare-hare ta sama da kasa.
A makon da ya gabata Isra'ila ta tura da wakilanta zuwa birnin Alkhahira, kuma dukannin bangarorin Palasdinawa, su ma sun aike da nasu wakilan a karkashin shiga tsakani na kasar Masar, wacce ke kokarin ganin bangarorin biyu sun sasanta domin samar da tsagaita wuta ta din-din-din.(Suwaiba)