Ranar 5 ga wata kungiyar tarayyar hadin kan Turai wato EU ta ce, duk da yake ta yi maraba matuka da tsagaita wuta da aka yi a zirin Gaza, to amma tana fatan tsagaita wutar na yanzu zai zama ginshikin samar da tsagaita wuta na din-din-din.
Wata sanarwa daga kungiyar EU, ta ce tana fatan dukkanin bangarorin dake rikici da juna za su girmama tsagaita wutar tare da yin biyayya ga sharuddan tsagaita wsutar.
Sanarwar ta ce, dole ne a kawo karshen asarar rayukan jama'a nan take, kuma kamar yadda kungiyar ta EU ta ce, lokaci ya yi da za a dakatar da harba rokoki a zirin Gaza.
Kungiyar EU ta kuma yaba da matakin da kasar Masar ta dauka na shiga tsakani domin samar da tsagaita wuta a yankin na zirin Gaza.(Suwaiba)