in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da musayar wuta tsakanin Palesdinu da Isra'ila
2014-07-31 10:47:59 cri

Wani jami'in hukumar kiwon lafiyar Palesdinu a zirin Gaza, ya ce wasu Bama-bamai da sojojin Isra'ila suka harba sun fada wata kasuwa dake yankin gabashin Sheja'eya dake zirin Gaza, lamarin da ya haddasa mutuwar Palesdinawa 17, baya ga wasu fiye da 160 da suka jikkata.

Jami'in ya kuma kara da cewa, lamarin ya faru ne cikin wa'adin tsagaita wuta na tsawon sa'o'i hudu da Isra'ila ta gabatar. Hakan dai na shaida yadda fada ke ci gaba da kazanta tsakanin tsagin Palesdinu da na Isra'ila har ya zuwa ranar Laraba.

A daya bangaren kuwa wata sanarwa da wani kakakin sojin Isra'ila ya fitar, ta ce sojojin Isra'ilan uku sun rasa rayukansu a yayin da ake dauki ba dadi a ranar Laraba.

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon dai ya yi tir da harin da aka kai wata makaranta dake zirin Gaza a ranar Talata, harin da ake zargin sojojin Isra'ila da aiwatarwa.

A wani ci gaban kuma, fadar shugaban kasar Algeria ta fidda wata sanarwa, dake cewa shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika ya amince da baiwa al'ummar zirin Gaza tallafin dalar Amurka miliyan 25. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China