Mr. Wu ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, hare-haren da aka kai a yankin sun haddasa asarar dukiyoyi da rayukan jama'a masu dimbin yawa, ana kuma fargabar mummunan tabarbarewar yanayin jin kai a yankin, lamarin da ya sa kasar Sin ta nuna bacin rai da damuwarta matuka kan yanayin da ake ciki a yankin a halin yanzu.
Mr. Wu ya kara da cewa, abin da ya kamata a gaggauta aiwatarwa yanzu shi ne tsagaita bude wuta a yankin ba tare da bata lokaci ba, yana kuma fatan bangarorin da rikicin ya shafa za su amsa kiran gamayyar kasa da kasa na dakatar da musayar wuta, kana da mayar da martani ga kokarin da ake yi kan aikin shiga tsakani.
A nasa bangaren, Mr. Meshaal ya bayyana cewa, Hamas ta yaba wa kasar Sin da matsayin da take dauka kan kiyaye 'yancin Falesdinawa, kana ta nuna godiya ga Sin da namijin kokarin da take yi wajen ganin a tsagaita bude wuta a tsakanin Falesdinu da Isra'ila da kuma sassauta matsalar jin kai a yankin Gaza. Bugu da kari, ya jaddada cewa, Hamas na fatan za a dakatar da hare-haren da ake kaiwa a yankin Gaza cikin hanzari tare da kawar da shingen da aka yi wa yankin na Gaza da kuma kiyaye hakkin Falesdinawa bisa doka. (Maryam)