in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hamas ta nuna shakku game da batun tsagaita bude wuta da Isra'ila ta sanar
2014-08-04 10:51:26 cri
Kungiyar Hamas ta al'ummar falasdinawa ta bayyana shakku game da sanarwar tsagaita bude wuta ta sa'o'i 7 da Isra'ila ta sanar.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin kungiyar ta Hamas Sami Abu Zuhri ya ce kungiyarsa ba ta da tabbashi kan kalaman mahukuntan Isra'ila, don haka ya ce kamata ya yi falasdinawa su yi hattara game da wannan batu na tsagaita wutar.

Tun da fari dai ma'aikatar tsaron Isra'ila ta bayyana tsagaita bude wutar ne a mafi yawan yankunan dake zirin Gaza, bisa abin da ta kira bada damar shigar da kayan agajin jin kai, tun daga karfe 7 na safe ya zuwa karfe 4 na yammacin ranar Litinin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China