Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane
Tsarin rarraba shiyyoyin hukumomi na kasar Sin
Tsarin mulkin kasa na jamhuriyar jama`ar kasar Sin ya tanadi cewa,ana rarraba shoyyoyin hukumomin kasar Sin kamar haka:
1) An rarraba kasar Sin kamar lardi da jiha mai tafiyar da harkokin kanta da birnin dake karkashin shugabancin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin kai tsaye.
2) An rarraba lardi da jiha mai tafiyar da harkokin kanta kamar shiyya mai tafiyar da harkokin kanta da gunduma da gunduma mai tafiyar da harkokin kanta da birni
3) An rarraba gunduma da gunduma mai tafiyar da harkokin kanta da birni kamar gari da garin kabilu
Jiha mai tafiyar da harkokin kanta da shiyya mai tafiyar da harkokin kanta da gunduma mai tafiyar da harkokin kanta su ne wuraren da kananan kabilu ke tafiyar da harkokin kansu.
Idan an ga tilas ne,gwamnatin kasar Sin tana iya kafa yankin hukuma ta musamman.
A halin da ake ciki yanzu,gaba daya kasar Sin tana da shiyyoyin hukumomi na matsayi na lardi 34,wadanda a ciki sun hada da birane 4 wadanda ke karkashin shugabancin gwamnatin tsakiya kai tsaye da larduna 23,jihohi masu tafiyar da harkokin kansu 5 da yankunan musamman 2.
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China |