>

Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane

Labarin kasa na kasar Sin
Kasar Sin wata kasa ce mai yawan duwatsu,fadin shiyyoyin tsaunukan kasar Sin ya kai kashi biyu bisa uku daga cikin kwatankwacin duk fadin kasa.A nan shiyyoyin tsaunuka sun hada da tsaunuka da tuddai da kananan duwatsu.A cikin labarin kasa iri-iri na kasar Sin,tsaunuka sun kai kashi 33 cikin dari,tuddai sun kai kashi 26 cikin dari,kwatarniya sun kai kashi 19 cikin dari,falalin kasa sun kai kashi 12 cikin dari,kananan duwatsu sun kai kashi 10 cikin dari.

Tun shekaru miliyoyi,tuddan Qingzang ya fito,wannan al`amari ne mai muhimmanci a kan tarihin duniya,wannan shi ma ya kago labarin kasa na kasar Sin.Daga sararin sama,ana iya ganin kasa mai fadi ta kasar Sin kuma ta yi kama da matakalu,daga yamma zuwa gabas,ta yi kasa kasa a kai a kai.Saboda dalilin yanayin kasa,tuddan Qingzang ya yi ta sama sama a kwana a tashi,matsakaicin tsawonsa ya fi tsawon leburin teku da mita dubu hudu,har ya fi tsayi a duniya,saboda haka ya zama matakala ta farko ta labarin kasa na kasar Sin.A kan tuddan Qingzang,babban dutsen Himalaya shi ne dutse mafi tsayi a duniya,tsawonsa ya fi tsawon leburin teku da mita dubu takwas da dari takwas da arba`in da takwas.Matakala ta biyu ta labarin kasa ta kasar Sin ta hada da tuddan Mongolia ta gida da tuddan rawayan kasa da tuddan Yungui da kwatarniyar Zhunger da kwatarniyar Sichuan,matsakaicin tsawonsu ya fi tsawon leburin teku da mita dubu daya ko dubu biyu.Daga gabashin matakala ta biyu wato dutsen Daxing`anling da dutsen Tai`ang da dutsen Wu da dutsen Xuefeng har zuwa gabar tekun Pasific dake gabashin kasar Sin,wannan matakala ta uku ta labarin kasa ta kasar Sin,tsawon wannan matakala ya fi tsawon leburin teku da mita dari biyar ko dubu daya kawai,daga arewa zuwa kudu,matakala ta uku ta hada da falalin kasa dake arewa maso gabashin kasar Sin da na Huabei da na gabar kogin Yangtse,kusa da falalin kasa,akwai kananan duwatsu da yawa.Daga gabashin matakala ta uku har zuwa ruwan teku,shi ne matakala ta hudu ta labarin kasa ta kasar Sin,zurfin ruwan bai kai mita dari biyu ba.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China