>

Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane


Yawan mutanen kasar Sin

Kasar Sin ita ce kasa mafi yawan mutane a duniya,ya zuwa shekarar 2002,kwatankwacin yawan mutanen kasar Sin sun kai milliyan dubu daya da dari biyu da tamanin da hudu da dubu dari biyar da talatin,wato ba su hada da na yankin musamman na Hongkong da na yankin musamman na Macao da na lardin Taiwan ba,yawan mutanen kasar Sin sun kai kashi 20 cikin dari na duk fadin duniya.A kasar Sin,kowane murabba`in kilomita akwai mutane 135,kuma yawan mutanen dake gabashin kasar Sin sun fi na yammacin kasar Sin yawa.A halin da ake ciki yanzu,matsakaicin tsawon rai na mutanen kasar Sin ya kai shekaru 71.40,wanda a ciki,tsawon rai na namiji ya kai shekaru 69.63,na mace ya kai shekaru 73.33,wannan ya fi na matsakaicin tsawon rai na mutanen duniya tsawo har da shekaru 5,idan an kwatanta shi da na kasashe da shiyyoyi masu tasowa,shi ma ya fin shi tsawo har da shekaru 7,amma idan an kwatanta shi da na kasashe masu ci gaba,to,ya fin shi kasawa har da shekaru 5.

A shekarar 2002,kashin karuwar yawan mutanen kasar Sin ya kara raguwa,ya zuwa karshen wannan shekara wato shekarar 2002,kwatankwacin yawan mutanen kasar Sin ya kai milliyan dubu daya da dari biyu da tamanin da hudu da dubu dari biyar da talatin,wadanda a ciki,yawan mutanen birane da garuruka sun kai milliyan dari biyar da biyu da dubu dari daya da ashirin,sun kai kashi 39.1 cikin dari na dukkan mutanen kasar Sin,yawan mutanen kauyuka na kasar Sin sun kai milliyan dari bakwai da tamanin da biyu da dubu dari hudu da goma,wato sun kai kashi 60.9 cikin dari.Yawan maza na duk fadin kasar Sin sun kai milliyan dari shida da sittin da daya da dubu dari daya da hamsin,yawan mata kuwa sun kai milliyan dari shida ashirin da uku da dubu dari uku da tamanin.Yawan yara wadanda shekarunsu da haihuwa suka kai shekaru kasa da goma sha hudu sun kai kashi 22.4 cikin dari na dukkan yawan mutanen kasar Sin.,yawan mutane wadanda shekarunsu da haihuwa ya kai shekaru tsakanin goma sha biyar da sittin da hudu sun kai kashi 70.3 cikin dari,tsofaffi wadanda shekarunsu da haihuwa suka kai shekaru fiye da sittin da biyar sun kai kashi 7.3 cikin dari,wato yawan tsofaffi na kasar Sin ya kai milliyan casa`in da uku da talatin da bakwai da dubu saba`in.A duk shekara,ana haihuwar yara milliyan goma sha shida da dubu dari hudu da saba`in a duk fadin kasar Sin,wato kashin haihuwa shi ne kashin 12.86 cikin dubu,yawan mutanen da suke mutuwa sun kai milliyan takwas da dubu dari biyu da goma,kashin mutuwa ya kai kashi 6.41 cikin dubu ;yawan mutanen da suke karuwa a duk shekara sun kai milliyan takwas da dubu dari biyu da sittin,kashin karuwar yawan mutane ya kai 6.45 cikin dubu.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China