>

Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane

Fadin kasar Sin

Jamhuriyar jama`ar kasar Sin,wato kasar Sin tana gabashin nahiyar Asiya kuma tana yammancin tekun Pasific.Fadin kasarta ya kai wajen muraba`in kilomita milliyan tara da dubu dari shida,kasar Sin ita ce kasa mafi girma a Asiya,a duk fadin duniya kuwa,kasar Sin ita ce kasa ta uku a bayan Rasha da Canada.
A arewa,yankin kasar Sin ya fara ne daga layin tsakiya na kogin Helongjiang dake arewancin Mohe,a kudu,ya fara ne daga Zengmu`ansha dake kudancin tsibirin Nansha,daga arewa zuwa kudu,nisansa ya kai wajen kilomita dubu biyar da dari biyar.A gabas,yankin kasar Sin ya fara ne daga wurin da kogin Helongjiang da kogin Wisuli suka hadu,a yamma,ya fara ne daga tuddan Pamil,daga gabas zuwa yamma,nisansa ya kai wajen kilomita dubu biyar.
Layin iyakar kasa na kasar Sin ya kai kusan kilomita dubu ashirin da biyu da dari takwas,a gabashinta ita ce Korea,a arewacinta ita ce Mongolia,a arewa maso gabashinta ita ce Rasha,a arewa maso yammacinta su ne Kazakhstan da Kyrghyz da Tajikstan,a yamma da kuma kudu maso yammacin kasar Sin su ne Afghanistan da Pakistan da Indiya da Nepal da Bhutan da sauransu,a kudu kuma su ne Myama da Laos da Vietnam.A gabas da kuma kudu maso gabashin kasar Sin,wato bayan teku su ne Korea ta kudu da Japan da Philipines da Brunei Darussalam da Malaysia da Indonesia.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China