Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane
Shiyyoyin hukumomi na matsayi na Lardi na kasar Sin
A halin da ake ciki yanzu,gaba daya kasar Sin tana da shiyyoyin hukumomi na matsayi na lardi 34,wato sun hada da larduna 23 da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu 5 da birane 4 da yankunan musamman 2.
Birane hudu wadanda ke karkashin shugabancin gwamnatin tsakiya kai tsaye sun hada da su:
Birnin Beijing
Birnin Beijing shi ne babban birnin jamhuriyar jama`ar kasar Sin,ana iya kiransa `Jing`,yana arewa maso yammancin yankin Huabei.A can can da,ana kiransa `Ji`,daga baya,ana kiransa `Yandu` da `Yanjing` da `birnin Du` da `Zhongdu` da `Dadu` da `Beiping` da `Beijing`.A shekarar 1928,aka kafa birni a Beijing.A karkashin shugabancinsa,akwai unguwoyi goma sha shida da gundumomi biyu,birnin Beijing shi ne birnin dake karkashin shugabancin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin kai tsaye.Fadin birnin Beijing ya kai murabba`in kilomita dubu goma sha shida da dari takwas.Ya zuwa karshen shekarar 2002,gaba daya `yan birnin Beijing sun kai milliyan goma sha daya da dubu dari uku da sittin da uku.Birnin Beijing shi ne cibiyar siyasa ta kasar Sin,kuma shi ne cibiyar al`adu da kimiyya da ba da ilmi da kuma sufuri.Ban da wannan kuma birnin Beijing shi ne ni`imtaccen wuri wanda ya yi suna a gida kasar Sin da kuma duk duniya,muhimman shahararrun ni`imtattun wurare na birnin Beijing sun hada da babbar ganuwa da fadar sarakuna da dakin ibada da kaburburan sarakuna goma sha uku da fadar sarki a lokacin zafi da dutsen Xiangshan da dai sauransu.
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China |