>

Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane

Duwatsu
A kasar Sin,akwai manyan duwatsu da yawa,kuma manyan duwatsu sun hada da duwatsu a jere,wadanda suka fi yin suna a kasar Sin sun hada da manyan duwatsu a jere na Himalaya da na Kunlun da na Tianshan da na Tanggula da na Qinling da na Daxin`anling da na Taihang da na Qilian da na Hengduan da dai sauransu.

To,yanzu bari mu yi muku bayani kan su filla filla.

Da farko dai,ga manyan duwatsu na Himalaya.Manyan duwatsu na Himalaya sun hada da manyan duwatsu a jere,suna zaune a kan iyakar yankin kasa dake tsakanin kasar Sin da Indiya da Nepal da sauran kasashe,tsawonsu ya kai fiye da kilomita dubu biyu da dari hudu,matsakaicin tsawonsu ya fi tsawon leburin teku da mita dubu shida,wato su ne duwatsu mafiya tsayi a duniya.Babban dutse mafi tsayi na manyan duwatsu na Himalaya wato babban dutsen Zhumolangma shi ne babban dutse mafi tsayi a duniya,wanda ake kira Everest da turanci,tsawonsa ya fi tsawon leburin teku da mita dubu takwas da dari takwas da arba`in da takwas.

To,yanzu sai manyan duwatsu na Kunlun.A yammancin manyan duwatsu na Kunlun ya fara ne daga tuddan Pamil,gabashinsu ya kai arewa maso yammancin lardin Sichuan na kasar Sin,tsawonsu ya kai kilomita fiye da dubu biyu da dari biyar,matsakaicin tsawonsu ya fi tsawon lebur din teku da mita dubu biyar har zuwa dubu bakwai,babban dutse mafi tsayi nasu shi ne dutsen Gongger,tsawonsa ya fi tsawon leburin teku da mita dubu bakwai da dari bawai da goma sha tara.

Yanzu sai manyan duwatsu na Tianshan.Manyan duwatsu a jere na Tianshan suna tsakiyar jihar Xingjiang ne mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kabilar Vigour dake arewa maso yammancin kasar Sin,matsakaicin tsawonsu ya fi tsawon leburin teku da mita dubu uku har zuwa dubu biyar,babban dutse mafi tsayi nasu shi ne dutsen Tuomur,tsawonsa ya fi tsawon leburin teku da mita dubu bakwai da dari hudu da hamsin da uku.

To,yanzu sai manyan duwatsu na Tanggula.Manyan duwatsu a jere na Tanggula suna tsakiyar tuddan Qingzang wato Qinghai da Tibet.Matsakaicin tsawonsu ya fi tsawon leburin teku da mita dubu shida,babban dutse mafi tsayi nasu shi ne dutsen Geladandong,tsawonsa ya fi tsawon leburin teku da mita dubu shida da dari shida da ashirin da daya,shi ne mafarin kogin Yangtse,wato kogi mafi tsawo na kasar Sin.

Yanzu sai manyan duwatsu na Qinling.Daga yammanci ya fara ne daga gabashin lardin Gansu na kasar Sin,ta gabashinsu ya kai yammancin lardin Henan na kasar Sin.Matsakaicin tsawonsu ya fi tsawon leburin teku da mita dubu biyu har zuwa dubu uku,babban dutse mafi tsayi nasu shi ne dutsen Taibai,tsawonsa ya fi tsawon leburin teku da mita dubu uku da dari bakwai da sittin da bakwai.

Yanzu sai manyan duwatsu na Daxin`anling.Arewancinsu ya fara ne daga kogin Mohe na lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin,kudancinsu ya kai kogin Laoha,tsawonsu ya kai kilomita dubu daya,matsakaicin tsawonsu ya fi tsawon leburin teku da mita dubu daya da dari biyar,babban dutse mafi tsayi nasu shi ne dutsen Huanggangliang,tsawonsa ya fi tsawon leburin teku da mita dubu biyu da ashirin da tara.

Yanzu ga bayani kan manyan duwatsu na Taihang.Manyan duwatsu na Taihang suna iyakar gabashin tuddan Huangtu wato rawayen kasa,tsawonsu ya kai fiye da kilomita dari hudu,matsakaicin tsawonsu ya fi tsawon leburin teku da mita dubu daya da dari biyar har zuwa dubu biyu,babban dutse mafi tsayi nasu shi ne dutsen karamin Wutai,tsawonsa ya fi tsawon leburin teku da mita dubu biyu da dari takwas da tamanin da biyu.

Yanzu kuma sai manyan duwatsu na Qilian,manyan duwatsu na Qilian suna iyakar arewa maso gabashin tuddan Qingzang wato Qianghai da Tibet,matsakaicin tsawonsu ya fi tsawon leburin teku da mita dubu hudu,tsawon babban dutse mafi tsayi nasu ya fi tsawon leburin teku da mita dubu biyar da dari biyar da arba`in da bakwai.

Yanzu ga bayani kan manyan duwatsu na Hengduan,manyan duwatsu na Hengduan suna kudu maso gabashin plateau Qingzang,wato suna wuraren dake hada jihar Tibet da lardin Sichuan da lardin Yunnan na kasar Sin.Matsakaicin tsawonsu ya fi tsawon leburin teku da mita dubu biyu har zuwa dubu shida,babban dutse mafi tsayi nasu shi ne dutsen Gongga,tsawonsa ya fi tsawon leburin teku da mita dubu bakwai da dari biyar da hamsin da shida.

Yanzu sai manyan duwatsu na Taiwan.Manyan duwatsu na Taiwan suna yankin dake gabashin tsibirin Taiwan na kasar Sin,matsakaicin tsawonsu ya fi tsawon leburin teku da mita dubu uku har zuwa dubu uku da dari biyar,babban dutse mafi tsayi shi ne dutsen Yushan,tsawonsa ya fi tsawon lebur din teku da mita dubu uku da dari tara da hamsin da biyu.

Ban da duk wadannan kuma,shahararrun duwatsu na kasar Sin sun hada da dutsen Huang da dutsen Tai da dutsen Hua da dutsen Song da dutsen Heng da dutsen Huan da dutsen Ermei da dutsen Lu da dutsen Wudang da dutsen Yandang da dai sauransu.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China