Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane
Dabbobin kasar Sin da rabe-rabensu
Kasar Sin ita ce kasa daya daga cikin kasashen duniya wadanda suka fi yawan ire-iren namun daji.A duk fadin kasar Sin,dabbobi da ake kira `vertebrate` wato masu kashin baya sun kai ire-ire guda 6266,wadanda a ciki,ire-iren dabbobi sun kai 500,tsuntsaye sun kai 1258,halittu masu rarrafe sun kai 376,dabbobi wadanda ke yin zaman rayuwa a kan kasa ko cikin ruwa sun kai 284,kifaye sun kai 3862,wato sun kai kashi 10 cikin dari na duniya.Ban da wannan kuma,dabbobi irin na `invertebrate` sun kai fiye da dubu hamsin,kwari kuwa sun kai dubu dari daya da hamsin.
A kasar Sin,ya kasance da dabbobi na musamman ir-iri da yawan gaske.Bisa kididdigar da aka yi,an ce,dabbobi irin na `vertebrate` masu kashin baya wadanda ke yin zaman rayuwa a kan kasa wajen 476 suna wuri daya wato a kasar Sin kawai.Namun daji masu daraja fiye da dari daya na kasar Sin sun yi suna sosai a duniya,wato sun hada da panda da biri mai launin zinariya da `tiger` na yankin Huanan na kasar Sin da gauraka mai jan kai da kada na kogin Yangtse dai sauransu.Manyan dabbobi masu ba da nono wanda ke da gashi mai launin fari da baki wato panda sun kai nauyin kilo 135,sun fi so su ci gora,a halin da ake ciki yanzu,yawansu ya kai wajen dubu daya kawai.Saboda suna da daraja kwarai da gaske,shi ya sa aka mayar da su a matsayin alama ta kare naman daji ta duniya.Gauraki masu jan kai kuwa,tsawon jikinsu ya kai fiye da mita 1.2,suna da gashi mai launin fari fat,a kansu,akwai wani wuri mai launin ja,a shiyyar dake gabashin Asiya,ana mayar da su a matsayin alamar `dogon rai`.
A kasar Sin,ana rarraba dabbobi a shiyyoyi bakwai wato sun hada da shiyyar arewa maso gabashin kasar Sin da ta Huabei da ta Mengxing da ta Qingzang da ta kudu maso yammacin kasar Sin da ta Huanan da ta huazhong,saboda yanayin kasa na wurare dabam daban ya sha banban juna,shi ya sa dabbobin wurare dabam daban su ma sun sha banban.
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China |