>

Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane


Haddin ruwa da tsibirori na kasar Sin
A arewa, layin gabar teku na babban yankin kasar Sin ya fara ne daga bakin kogin Yalujiang na lardin Liaoning,a kudu,ya fara ne daga bakin kogin Beilun na jihar Guangxi,gaba daya tsawonsa ya kai wajen kilomita dubu goma sha takwas.A gabar teku,tasoshin dake da sharuda masu kyau suna da yawan gaske,wadanda a ciki,yawancinsu su ne ba su daskare ba a duk shekara.Tekun dake kusa da yankin kasar Sin sun hada da tekun Bohai da rawayan teku da gabashin teku da kudancin teku da tekun Pasific dake gabashin lardin Taiwan na kasar Sin.A ciki,tekun Bohai yana cikin yankin kasar Sin.A arewa,tekun Pasific dake gabashin lardin Taiwan ya fara ne daga tsibirorin Xiandao dake kudu maso yammancin tsibirorin Liuqiu na Japan,a kudu,ya fara ne daga hancin teku na Bashi.

Shiyyoyin teku ta kasar Sin sun hada da shiyyoyin teku na gida na kasar Sin da haddin ruwa na kasar Sin,kwatankwacin fadinsu sun kai fiye da muraba`in kilomita dubu dari uku da tamanin.Shiyyoyin teku na gida na kasar Sin sun hada da shiyyoyin tekun dake tsakanin layin gabar teku na kasar Sin da layin hadin ruwa na jamhuriyar jama`ar kasar Sin.Daga shatin iyaka na haddin ruwa,fadin haddin ruwa na kasar Sin ya kai mil na teku goma sha biyu.

A kan shiyyoyin teku na kasar Sin,gaba daya ya kasance da tsibirori fiye da dubu biyar,kwatankwacin fadinsu ya kai wajen muraba`in kilomita dubu tamanin,shatin iyakar gabar teku na tsibirori ya kai kusan kilomita dubu goma sha hudu.Daga cikinsu,tsibirin Taiwan ya fi girma,fadinsa ya kai murabba`in kilomita dubu talatin da shida,na biyu shi ne tsibirin Hainan,fadinsa ya kai muraba`in kilomita dubu talatin da hudu.Tsibirin Diaoyu yana arewa maso gabashin tsibirin Taiwan na kasar Sin,shi ne tsibiri mai nisa na gabashin kasar Sin.A kan kudancin teku,akwai tsibirori da yawa,ana kiransu tsibirorin Nanhai wato kudancin teku ke nan,suna wuri mai nisa na kudancin kasar Sin ne,kuma sun hada da tsibirori hudu wato tsibirorin Dongsha da na xisha da na zhongsha da kuma nansha.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China