>

Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane


Albarkatan kasa
Kasar Sin kasa ce mai kyau,tana da kasa mai fadi kuma albarkatan kasa na kasar Sin suna nan da iri-iri masu yawan gaske,alal misali,gona da kungurmin daji da yanki mai ciyayi da dajin gona da wurin da ruwa ba shi da zurfi.Amma a kasar Sin,tuddai sun yi yawa,fadin kasa ba shi da yawa,gonaki da kungurmin daji su ma ba su da yawa.Kuma yawancin gonaki suna kasa na gabashin kasar Sin,yawancin kungurmin daji suna tsaunuka dake arewa maso gabashin kasar Sin da kudu maso yammancin kasar Sin,yawancin yanki mai ciyayi suna tuddai da tsaunuka na yammancin kasar Sin.

Yanzu ga bayani kan gonaki na kasar Sin.Gaba daya gonakin kasar Sin sun kai muraba`in kilomita milliyan daya da dubu dari biyu da saba`in,a gabashin kasar Sin da yammancin kasar Sin,gonaki ba su da yawa,amma a tsakiyar kasar Sin,gonaki sun yi yawa har sun kai kashi 43.2 cikin dari daga dukkan gonaki na kasar Sin.Wato yawancin gonakin kasar Sin suna kan kasa na Dongbei wato suna arewa maso gabashin kasar Sin da kan kasa na Huabei wato gabashin kasar Sin da na gabar kogin Yangtse da mashigin bakin takun Zhujiang da kwatarniyar Sichuan.Launin kasa na kan kasa na arewa maso gabashin kasar Sin shi ne baki,mutanen wurin su kan dasa alkama da masara da dawa da maiwa da wake da rama.Launin kasa na gabashin kasar Sin shi ne launin ruwan kasa,mutanen wurin su kan dasa alkama da masara da hatsi da dawa da auduga da gyada.A kwatarniyar Schuan,mutane su kan dasa shinkafa da rake da shayi da lemu da sauransu.

Yanzu ga bayani kan kungurmin daji na kasar Sin.A halin da ake ciki yanzu,kwatankwacin fadinsu ya kai hekta milliyan dari daya da hamsin da tara da dubu dari tara da arba`in,kashin rufewar kungurmin daji ya kai kashi 16.55 cikin dari,wato bai yi yawa ba.Yawancin halitattun kungurmin daji na kasar Sin suna shiyyar arewa maso gabashin kasar Sin da kuma shiyyar kudu maso yammancin kasar Sin.

Bishiyoyi na kungurmin daji na kasar Sin suna nan iri iri masu yawan gaske,bishiyoyi masu tsayi kawai sai sun riga sun kai fiye da iri-iri dubu biyu da dari takwas.Don kiyaye muhalli da kuma biyan bukatun gine-ginen tattalin arziki,kasar Sin ta nuna kwazo da himma don dasa bishiyoyi bisa babban mataki.Yanzu,fadin kungurmin daji da aka dasa na kasar Sin ya riga ya kai hekta milliyan talatin da uku da dubu dubu dari bakwai da casa`in,wato kasar Sin ta riga ta zama kasa mafi yawan kungurmin daji da aka dasa a duniya.

Muhimman shiyyoyin kungurmin daji na kasar Sin sun hada da shiyyoyi uku wato su ne : na farko,shiyyar kungurmin daji dake arewa maso gabashin kasar Sin,wadanda a ciki sun hada da dutsen Daxing`anling da dutsen Xiaoxing`anling da dutsen Changbai,wannan shiyya ita ce shiyyar halitattun kungurmin daji mafi girma na kasar Sin.Na biyu,shiyyar kungurmin daji dake kudu maso yammancin kasar Sin,wadanda a ciki sun hada da tsaunukan Hengduan da kungurmin daji dake karkashin duwatsun Himalaya da kungurmin daji dake gabar kogin Yaluzangbu,wadannan su ne halitattun kungurmin daji mafi girma ta biyu ta kasar Sin.Na uku,shiyyar kungurmin daji dake kudu maso gabashin kasar Sin,suna kudancin dutsen Qingling da kogin Huaihe,kuma suna gabashin tuddan Yungui,su ne shiyyar kungurmin daji mafi muhimmanci da aka dasa a kasar Sin.Ban da wannan kuma,a kasar Sin,mutane sun taba dasa wani zirin kungurmin daji mai kiyaye muhalli,wanda ya fi tsawo ya kai kilomita fiye da dubu bakwai,wato fadinsa ya kai hekta milliyan dari biyu da sittin,ana kiran shi da sunan `babban aikin halittu masu rai da marasa rai a duniya`.

Yanzu ga bayani kan yanki mai ciyayi.A kasar Sin,fadin yanki mai ciyayi ya kai hekta milliyan dari biyu da sittin da shida da dubu sittin,kuma suna nan iri-iri masu yawan gaske,ana iya yin amfani da su a lokuta dabam daban.Fadin yanki mai ciyayi na kasar Sin ya kai kashi wajen 25 cikin dari in an kwatanta shi da na duk fadin kasar Sin,wato kasar Sin ita ce daya daga cikin kasashe wadanda suka fi yawan yanki mai ciyayi.Yawancin halitattun yankuna masu ciyayi na kasar Sin suna shiyoyi masu fadi dake yamma maso arewancin dutsen Daxing`an da dutsen Ying da kuma tuddan Qingzang,yanki mai ciyayi da aka dasa kuma yawancinsu suna shiyoyin dake kudu maso gabashin kasar Sin,wato suna hada da gonaki da kungurmin daji.

Muhimman kasar makiyaya ta kasar Sin sun hada da kasar makiyaya ta Mongolia ta gida da kasar makiyaya ta Xinjiang da kasar makiyaya ta Qinghai da kasar makiyaya ta Tibet.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China