>

Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane


Shuke-shuken kasar Sin da rabe-rabensu
Kasar Sin ita ce daya daga cikin kasashe masu yawan albarkatan shuke-shuke a duniya,yawan shuke-shukenta sun kai fiye da dubu talatin,wato ta kai matsayi na uku a duniya,Malaysia da Brazil sun kai matsayi na farko da na biyu,wadanda a ciki `bryophyte` sun kai iyalai 106,sun kai kashi 70 cikin dari na duniya;`pteridophyte` sun kai iyalai 52,sun kai kashi 80 cikin dari na duniya,kuma ire-irensu sun kai dubu biyu da dari shida,sun kai kashi 26 cikin dari na duniya.Yawan `bishiyoyin katako` na kasar Sin sun kai iri-iri har dubu takwas,wadanda a ciki bishiyoyi masu tsayi sun kai dubu biyu.

Kasar Sin da tana shuke-shuken musamman nata da yawa,alal misali,`metasequoia` da `china cypress` da ` ginkgo` da `china fir` da `Taiwan fir` da `cypress na Fujian` da `dove tree` da `eucommia` da sauransu.A cikinsu,`metasequoia` shi ne irin wata bishiya mai tsayi sosai,ana mayar da shi a matsyain shuke-shuke mafi daraja,kuma ba su da yawa a duniya.Shuke-shuken da ake ci a kasar Sin sun kai iri-iri fiye da dubu biyu,shuke-shuken da ake yin amfani da su wajen yin magunguna sun kai dubu uku.`Ginseng` na dutsen Changbai da `safflower` na Tibet da `lycium chinense` na lardin Ningxia da `pseudo-ginseng` na lardin Yunnan da lardin Guizhou dukkansu magunguna ne masu daraja.Ban da wannan kuma,shuke-shuken furanni na kasar Sin su ma suna da yawan gaske,alal misali,sarauniyar furanni wato `peony` ana samunta tana wuri daya wato kasar Sin kawai.`Peony` tana da kyaun gani kwarai da gaske,launinta shi ma yana da kyaun gani kwarai da gaske,ana mayar da ita a matsayin daya daga cikin `furannin kasa` na kasar Sin.

Kungurmin daji na kasar Sin su ma suna nan iri-iri dabam daban.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China