>

Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane

Birnin Chongqing
Ana iya kiran birnin Chongqing `Yu`,yana gabashin shiyyar kudu maso yammancin kasar Sin,wato mafarin kogin Yangtse.A lokacin da ake yin yaki da masu kai hari na Japannawa,birnin Chongqing shi ne babban birni na gwamnatin jam`iyyar `Guomindang`.A shekarar 1997,aka kafa birnin Chongqing wanda ke karkashin shugabancin gwamnatin tsakiya kai tsaye,birnin Chongqing na yanzu ya hada da tsohon birnin Chongqing na lardin Sichuan da birnin Wanxian da birnin Fuling da kuma shiyyar Qianjiang.A karkashinsa,akwai gundumomi 15 da birane na matsayin gunduma 4 da gundumomi 17 da gundumomi masu ikon tafiyar da harkokin kansu 4.Fadinsa ya kai murabba`in kilomita dubu tamanin da biyu da dari uku.Ya zuwa karshen shekarar 2002,gaba daya `yan birnin Chongqing sun kai milliyan talatin da daya da dubu saba`in.Birnin Chongqing shi ne hadadden birnin masana`antu.Shahararrun ni`imtattun wurarensa sun hada da `Sanxia` na kogin Yangtse da detsen Pipa da dutsen Jinyun da sauransu.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China