Liu Xiabing mai shekaru 31 da haihuwa, ‘yar asalin garin Pingnan na gundumar Lingshan ta larin Guangxi dake kudu maso yammacin kasar Sin ce. Kayayyakin da ake sakawa da gora na Lingshan sanannu ne, kuma ana sayar da su a kasashen waje, kuma a da sun taba kasancewa tushen samun kudin shiga na jama'ar wurin. Bayan rikicin hada-hadar kudi da ya barke a shekarar 2008, sana’ar saka da ake amfani da gora ta Lingshan, ita ma ta soma komawa baya sannu a hankali......
Ranar Lahari 22 ga watan Janairu, rana ce ta farko a cikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta al’ummar kasar Sin, wato shekarar Zomo. A halin yanzu al’ummar kasar na bukukuwa kala-kala domin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiyarsu. Wakilin mu Murtala Zhang ya samu damar zantawa da wasu daga cikin ‘yan kasashen Najeriya da Nijar dake zaune a wurare daban-daban na kasar Sin......
Bikin bazara wato Spring Festival a Turance, bikin gargajiya ne mafi kasaita ga Sinawa, da ke alamanta shiga sabuwar shekara bisa kalandar wata ta gargajiya ta kasar. Bikin bazara na kasar Sin yana da tsawon tarihin da ya kai kimanin shekaru 4000, kuma ya yi daidai da muhimmancin bikin Kirismeti ga Turawa, shi ne kuma biki mafi muhimmanci ga Sinawa.
Sinawa na da wata al’adar gargajiya ta kirga shekaru da dabbobi, kuma dabbobi 12 ne ake amfani da su, wato Bera, da Saniya, da Damisa, da Zomo, da Dragon, da Maciji, da Doki, da Tunkiya, da Biri, da Kaza, da Kare da kuma Alade, kuma ana zagaya duk dabbobin a shekaru 12.