Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane
Taken kasar Sin
Taken jamhuriyar jama`ar kasar Sin: taken jamhuriyar jama`ar kasar Sin shi ne `jarumai sun yi maci`.An rubuta shi a shekarar 1935,Mr.Tianhan ne ya rubuta kalmominsa,Mr.Nie`er ya rubuta takensa.An taba yin amfani da wannan waka a cikin wani wasan film da aka dauka a can can da,sunan wannan wasan filma shi ne `jarumai`,labarin dake shafar wannan wasan film shi ne kamar haka: a shekarar 1931,bayan ran 18 ga watan Satumba,Japan ta mamaye larduna uku dake arewa maso gabashin kasar Sin,al`ummar kasar Sin tana cikin wahala mafi tsanani,wasu dalibai sun shiga yaki.Bisa yaduwar wannan film,wakar ita ma ta yi ta yaduwa a duk fadin kasar Sin cikin sauri.
《 Taken Jamhuriyar Jama`ar Kasar Sin》
Tashi, jama`a wadanda ba su so su zama bayi,
Bari mu gina sabuwar babbar ganuwa da jini da naman jikinmu!
Al`ummar kasar Sin tana cikin hadari mafi tsanani,
Kowanenmu ya yi ruri kamar damisa,
Tashi! Tashi! Tashi!
Mu gama kai,mu yi maci a gaban wutar igogin makiya,
Mu yi maci a gaban wutar igogin makiya.
Macin gaba! Macin gaba! Macin gaba!
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China |