Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane
Manufar yin haihuwa cikin shiri ta kasar Sin
Kasar Sin tana aiwatar da manufar yin haihuwa cikin shiri,wato gwamnatin kasar Sin ta ba da jagoranci,mutanen kasar Sin kuma suna aiwatar da wannan manufa bisa sa kai.Gwamnatin tsakiya da kananan gwamnatocin wurare dabam daban sun tsara tsari da kuma kafa dokoki don kayyaden karuwar yawan mutanen kasa da daga ingancin mutanen kasa da kuma kyautata tsarin yawan mutanen kasa,kuma sun gabatar da aikin hidima ga mutane masu daura aure.Bisa sa kai ne mutanen kasar Sin suna yin haihuwa cikin shiri.
Muhimman abubuwan dake shafar manufar yin haihuwa cikin shiri ta kasar Sin sun hada da su: ya fi kyau a yi aure bayan shekaru 25 da haihuwa,ya fi kyau wani iyali ya haifi yaro daya kawai.A shiyyoyin kauyuka,yaran da kowanen iyali ya haifi ba za su iya wuce biyu ba.A shiyyoyin kananan kabilu kuwa,ana iya tsara tsarin yin haihuwa bisa halaye iri dabam daban.
Tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin haihuwa cikin shiri,a kai a kai ne yawancin mutanen kasar Sin suna karbanta bisa sa kai.A sa`i daya kuma manufar yin haihuwa cikin shiri ita ma ta taimakawa matan kasar Sin da su guje daga aiki na nauyi na yin haihuwa sau tarin yawa,daga nan lafiyar jikin mahaifiya da jariri ta sami kyautatuwa bisa babban mataki.
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China |