Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane
Yankunan musamman biyu sun hada da su:
Hongkong
Tun daga ran 1 ga watan Yuli na shekarar 1997 ne kasar Sin ta komo da Hongkong a karkashin mulkinta,kuma ta kafa yankin musamman na Hongkong wato `Gang`.Hongkong yana gabar teku ta kudu,wato gabashin mashigin teku na kogin Zhujiang.Hongkong yana kudancin birnin Shenzhen na lardin Guangdong,ya hada da tsibirin Hongkong da Jiulong da Xinjie da sauran kananan tsibirorin dake kusa da su,fadinsa ya kai murabba`in kilomita dubu daya da casa`in da takwas.Ya zuwa karshen shekarar 2002,gaba daya `yan yankin Hongkong sun kai milliyan shida da dubu dari takwas da goma sha biyar da dari takwas,wadanda a ciki zaunannun mazaunan yankin Hongkong sun kai milliyan shida da dubu dari shida da ashirin da biyar da dari uku.Sauransu sun kai dubu dari daya da casa`in da dari biyar.
Macao
Tun daga ran 20 ga watan Satumba na shekarar 1999,kasar Sin ta komo da Macao a karkashin mulkinta,kuma ta kafa yankin musamman na Macao wato `Ao`.Macao yana kan wata peninsular dake yammancin gabar kogin Zhujiang,ya hada da tsibirin Dangzai da tsibirin Luhuan,fadinsa ya kai murabba`in kilomita ashirin da biyar da digo takwas.Ya zuwa karshen shekarar 2002,mutanen dake zaune a Macao sun kai dubu dari hudu da arba`in da biyu.
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China |