>

Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane


Birnin Tianjin
Ana iya kiran birnin Tianjing `Jing`,yana arewa maso gabashin yankin Huabei,kuma yana wurin da kogin Haihe ya shiga tekun Bohai.A can can da,ana kiran birnin Tianjing `Zhigu`,shi ne muhimmin wurin da ana jigilar kayayyaki ta hanyar ruwa.Daga baya,aka kafa garin Haijing a nan.Tun daga farkon Daular Ming,sai aka fara kiransa `Tianjing`.A shekarar 1928,aka kafa birni a nan,a karkashinsa,akwai unguwoyi goma sha biyar da gundumomi uku,birnin Tianjing shi ne birnin dake karkashin shugabancin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin kai tsaye.Fadinsa ya kai murabba`in kilomita dubu goma sha daya.Ya zuwa karshen shekarar 2002,`yan birnin Tianjing sun kai milliyan tara da dubu hamsin.Birnin Tianjing shi ne wani babban birni na masana`antu,yana da albarkatan man fetur da gas da gishirin teku,kuma yana da tushe mai kyau na fasahar masana`antu.Birnin Tianjing shi ne muhimmiyar cibiyar kasuwanci ta arewancin kasar Sin.shahararrun ni`imtattun wuraren birnin Tianjing sun hada da lambunan shan iska na `Ning` da fadar `Tianhong` da tashar madafu ta Dagukou da dakin ibada na `Dule` dake gundumar Ji.Kazalika,ni`imtaccen wuri na `Panshan` shi ma ya yi suna sosai.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China