>

Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane


Albarkatan karfin iska da karfin ruwa da makamashin hasken rana
A kan yankuna masu fadi na kasar Sin,koguna suna da yawan gaske,ruwan kogi ma na da yawan gaske,nisan zubar ruwa na kogunan kasar Sin ya yi girma kwarai da gaske,ana iya cewa,kasar Sin tana da albarkatan makamashin ruwa masu yawa.An kimmanta cewa,yawan adanannun albarkatan makamashin ruwa na kogunan kasar Sin sun kai kilowaz milliyan dari shida da tamanin,kowace shekara yawan lantarkin da aka bayar ta hanyar yin amfani da makamashin ruwa ya kai kilo waz awa billiyan dubu dari tara da ashirin,yawan adanannan makamashin ruwa da za a yi amfani da su sun kai kilo waz milliyan dari uku da saba`in da takwas,kowace shekara yawan lantarkin da za a bayar da su ta hanyar yin amfani da makamashin ruwa za su kai kilo waz awa billiyan dubu daya da dari tara da ashirin.Ko yawan ajiye na albarkatan makamashin ruwa ko albarkatan makamashin ruwa da za a yi amfani da su na kasar Sin sun kai matsayi na farko a duniya.

A kasar Sin,yawan adanannan makamashin iska wanda tsayinsu ya kai mita goma sun kai kilo waz billiyan uku da milliyan dari biyu da ashirin da shida,an kimmanta cewa,yawan adanaddan makamashin iska dake kan kasa ya kai kilo waz milliyan dari biyu da hamsin da uku,albarkatan karfin iska na shiyyoyin dake kusa da teku wato zurfin ruwa ya kai fiye da mita goma sha biyar sun kai ninki uku na yawan adanannun kan kasa wato sun kai kilo waz milliyan dari bakwai da hamsin.Shiyyoyi wadanda ke mallakar makamashin iska da yawa na kasar Sin sun hada da yankin dake arewa maso yammacin kasar Sin da yankin Huabei da yanki mai ciyayi da yankin daji na gabashin kasar Sin da shiyyoyin dake gabar teku da tsibirori dake yankin gabas da yankin kudu maso gabashin kasar Sin.A dukkan wadannan wurare,iska ta yi karfi a lokacin bazara da lokacin sanyi,amma ruwan sama ya ragu;a lokacin zafi kuwa,karfin iska ya ragu,amma ruwan sama ya kara karuwa,ana iya ba da lantarki ta hanyar yin amfani da karfin iska.Ya zuwa karshen shekarar 1998,tasoshin ba da lantarki ta hanyar yin amfani da iska sun kai wajen ashirin a kasar Sin,wanda a ciki ya fi girma shi ne tashar ba da lantarki ta hanyar yin amfani da iska ta birnin Daban na jihar Xinjiang.Kasar Sin tana da makoma mai haske wajen bunkasa sha`anin yin amfani da makamashin iska.

Kasar Sin tana da albarkatan makamashin hasken rana da yawa,kowace shekara,makamashin hasken rana a kan kasa sun yi kama da makamashin kwal masu yawan ton billiyan dubu biyu da dari hudu,musamman ma a shiyyar dake arewa maso yammacin jihar Tibet.An kafa babbar tasha mai ba da lantarki ta hanyar yin amfani da makamashin hasken rana ta farko ta kasar Sin ne a kauyen Guligutai na shiyyar Gubalinyou ta jihar Mongolia ta gida,ta fara aiki ne tun daga ran 11 ga watan Oktoba na shekarar 1982.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China