Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane
Birnin Shanghai
Ana iya kiran birnin Shanghai `Hu`,birnin shanghai yana tsakiyar gabar tekun gabashin kasar Sin wato yana wurin da kogin Yangtse ya shiga teku.A can can,birnin Shangha wani karamin kauyen kamu kifaye ne dake kusa da gabar teku.Tun daga Daular Song,sai aka kafa wani gari a wurin,kuma aka fara kiransa `Shanghai`.Yanzu birnin shanghai shi ne daya daga cikin birane hudu wadanda ke karkashin shugabancin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin kai tsaye,a karkashinsa,akwai unguwoyi goma sha takwas da gunduma daya.Fadinsa ya kai murabba`in kilomita dubu biyar da dari takwas.Ya zuwa karshen shekarar 2002,`yan birnin Shanghai sun kai milliyan goma sha uku da dubu dari uku da arba`in da bakwai.Birnin Shanghai shi ne birni mafi girma a kasar Sin,shi me daya daga cikin manyan birane na duniya.Ban da wannan kuma,birnin shanghai shi ne birnin masana`antu mafi girma na kasar Sin kuma shi ne cibiyar kasuwanci da kudi da kuma sansanin kimiyya da fasaha.
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China |