>

Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane

Koguna
Kamar yadda kuka sani,akwai koguna da yawan gaske a cikin yankin kasar Sin,yawan kogunan da fadin hanyoyin ruwansu suka kai fiye da muraba`in kilomita dubu daya sun wuce dubu daya da dari biyar,kuma yawancin kogunan kasar Sin su zuba a cikin teku,wato fadin honyoyin ruwansu suka kai kashi 64 cikin dari dake cikin kwatankwacin fadin yankin kasar Sin.Alal misali,kogin Yangtse da Rawayen kogi da kogin Helongjiang da kogin Zhujiang da kogin Liaohe da kogin Haihe da kogin Huaihe da sauran koguna su zuba a cikin tekun Pasific.Kogin Yaluzangbujiang dake jihar Tibet,daya daga cikin jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin ya zuba a cikin tekun Indya,wato ya wuce daga babban kwazazzabi na Yaluzangbujiang.Wannan kwazazzabi shi ne kwazazzabi mafi girma a duniya,tsawonsa ya kai kilomita dari biyar da hudu digo shida,zurfinsa kuwa ya kai mita dubu shida da tara.Ban da wannan kuma kogin Erqisihe dake jihar Xinjiang na kabilar Vigour mai tafiyar da harkokin kanta ya zuba a cikin tekun Arctic.Ban da irin wannan kogi,sauran koguna su zuba a cikin tafki ko hamada.

Kogin Yangtse shi ne kogi mafi tsawo a kasar Sin,wato tsawonsa ya kai kilomita dubu shida da dari uku,ya kai matsayi na uku a bayan kogin Nile na Afirka da kogin Amazon na kudancin Amurka a duniya.Kuma yana da albarkatan ruwa mai arziki.Kogin Yangtse shi ma yana da babban amfani a fannin sufuri a kasar Sin.kazalika yanayin shiyyoyin dake kewayan kogin Yangtse yana da kyau wato ba zafi ba sanyi,ruwan sama kuma ya yi yawan gaske,gonakin wadannan shiyyoyi suna da ni`ima kwarai da gaske,shi ya sa an sami ci gaba da saurin gaske wajen masana`antu da sha`anin noma a wadannan shiyyoyi.

Rawayen kogi shi ne kogi na biyu mafi tsawo a kasar Sin,tsawonsa ya kai kilomita dubu biyar da dari hudu da sittin da hudu.Makiyaya dake hanyoyin ruwa na Rawayen kogi tana da ni`ima kwarai da gaske,albarkatan ma`adinai na wadannan wurare suna da arziki.A kan tarihi,shiyyar hanyoyin ruwa na Rawayen kogi shi ne daya daga cikin wuraren wayin kai na kasar Sin na zamanin da.

Kogin Helongjiang shi ne babban kogi dake arewancin kasar Sin,tsawonsa ya kai kilomita dubu hudu da dari uku da hamsin.A ciki,kogi mai tsawon kilomita dubu uku da dari daya da daya yana zubawa a cikin yankin kasar Sin.

Kogin Zhujiang shi babban kogi dake kudancin kasar Sin,tsawonsa ya kai kilomita dubu biyu da dari biyu da goma sha hudu.

Kogin Talimu dake kudancin jihar Xinjiang shi ne kogi mafi tsawo wanda bai zuba a cikin teku ba a kasar Sin,tsawonsa ya kai kilomita dubu biyu da dari daya da saba`in da tara.

Ban da kogunan hallita,akwai wani kogin da aka haka a nan kasar Sin,wato shi ne `Dayunhe`.An fara haka shi ne tun daga karni na biyar daga nan birnin Beijing har zuwa birnin Hangzhou na jihar Zhejiang dake kudancin kasar Sin,ya hada kogin Haihe da Rawayen kogi da kogin Huaihe da kogin Yangtse da kogin Qiantang,tsawonsa ya kai kilomita dubu daya da dari takwas da daya,`Dayunhe` na kasar Sin shi ne kogin da aka haka mafi tsoho kuma mafi tsawo a duniya.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China