>

Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane


Albarkatan ma`adinai na kasar Sin
Kasar Sin tana da albarkatan ma`adinai da yawan gaske,ya kai kusan kashi 12 cikin dari na dukkan albarkatan ma`adinai na duk duniya,wato kasar Sin ta kai ta uku a duniya.Amma saboda mutanen kasar Sin sun fi yawa a duniya,shi ya sa yawan albarkatan ma`adinai da kowanen mutumin kasar Sin ya mallaka ya kai kashi 58 cikin dari da kowanen mutum ya mallaka a duniya kawai,wato ya kai na 53 a duniya.Ya zuwa yanzu,gaba daya yawan ma`adinan da aka tarar da su sun riga sun kai 171,wadanda a ciki,ma`adinan da aka tarar da yawan ajiyansu sun kai 158,wato ma`adinan makamashi sun kai 10,ma`adinan karafan tama sun kai 5,ma`adinan karafa marasa tama sun kai 41,ma`adinan karafa masu tsada sun kai 8,ma`adinan da ba na karfe ba sun kai 91,sauran ma`adinai sun kai 3.Kasar Sin tana da fifiko wajen mallakar albarkatan ma`adinai.Kuma yawan adanannun muhimman ma`adinai goma sha biyu na kasar Sin sun kai lambawan a duniya,wato sun hada da karfen `rare-earth` da `gypsum` da `vanadium` da `titanium` da`tantalum` da `tungsten` da `bentonite` da `graphite` da `mirabilite` da `barite` da `magnesite` da `antimony` da ake kiransu haka a turance.

Halin rarraba albarkatan ma`adinai na kasar Sin shi ne kamar haka :yawancin man fetur da gas suna yankin arewa maso gabashin kasar Sin da yankin Huabei da kuma yankin arewa maso yammacin kasar Sin.Yawancin kwal suna yankin Huabei da yankin arewa maso yammacin kasar Sin.Yawancin tama suna yankin arewa maso gabashin kasar Sin da yankin Huabei da kuma yankin kudu maso yammacin kasar Sin.Yawancin tagulla suna yankin kudu maso yammacin kasar Sin da yankin arewa maso yammacin kasar Sin da yankin Huadong.Ma`adinan `lead` da `zinc` da ake kiransu haka a turance suna duk fadin kasar Sin.Yawancin `tungsten` da `kuza` da `molybdenum` da `antimony` da karfen `rare-earth` da ake kiransu haka a turance suna yankin Huanan da yankin Huabei.Ma`adinan zinariya da azurfa suna duk fadin kasar Sin,lardin Taiwan ta kasar Sin ita ma tana da ma`adinan zinariya da azurfa da yawa.Ban da wannan kuma yawancin ma`adinin `phosphorus` da ake kiransa haka a turance suna yankin Huanan na kasar Sin.

Muhimman albarkatan ma`adinai na kasar Sin sun hada da su :

Kwal : yawan ajiyen kwal na kasar Sin ya kai matsayi na farko a duniya,yawan adanannen da aka riga aka tarar da su a duk fadin kasar Sin sun kai ton billiyan dubu daya,yawancinsu suna yankin Huabei da shiyyar dake arewa maso yammacin kasar Sin,musamman ma suna lardin Shanxi da lardin Shaanxi da jihar Mongolia.

Man fetur da gas : yawancinsu suna shiyyar dake arewa maso yammacin kasar Sin.Ya zuwa karshen shekarar 1998,an riga an kafa filayen man fetur 509 da filayen gas 163.Yawan adanannen man fetur ya kai ton billiyan goma sha tara da milliyan dari takwas da hamsin,wannan ya kai matsayi na tara a duniya,na gas kuwa sun kai cubic mita billiyan dubu daya da dari tara da hamsin,shi ma ya kai matsayi na 20 a duniya.Muhimman manyan filayen man fetur da gas na kasar Sin sun hada da filaye shida wato su babban fili na Songliao da na tekun Bohai da na Talimu da na Zhunger da Tulufan da na Sichuan da na Shaangannin.

Ma`adinan karafa wato karafan tama da karafa marasa tama :

Karafan tama : karafan tama na kasar Sin sun hada da tama da `manganese` da `vanadium` da `titanium` da dai sauransu,wadanda a ciki yawan adanannen tama ya kai kusan ton billiyan hamsin,yawancinsu suna lardin Liaoning da lardin Hebei da lardin Shanxi da lardin Sichuan da sauran larduna.

Karafa marasa tama : kasar Sin ta mallaki dukkan ire-iren karafa marasa tama da aka tarar da su a duniya,wadanda a ciki yawan ajiye na karfe `rare-earth` na kasar Sin sun kai kashi 80 cikin dari na dukkan yawan adanannunsu a duk duniya,yawan ajiye na ma`adinin `antimony` na kasar Sin sun kai kashi 40 cikin dari na duniya,ma`adinin `tungsten` kuwa sun kai kashi 25 cikin dari.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China