Wani jirgin saman fasinja na kamfanin zirga-zirga na Asiya mai lamba QZ8501 ya bace tare da fasinjoji 162 , wanda aka kasa tuntubarsa daga cibiyar ba da umurni ga jiragen sama, bayan da ya tashi daga kasar Indonesiya a ranar Lahadi 28 ga wata ya nufi kasar Singapore. Bayan abkuwar lamarin, kasashen Indonesiya, Malaysiya, Singapore sun fara gudanar da aikin ceto nan da nan, ko da har yanzu ba a gano inda jirgin yake ba.
Ya zuwa yanzu, Indonesiya ce ke jagorantar aikin ceto. Masu kula da aikin ceto da sojojin Indonesiya suna kokarin neman jirgin a ruwan tekun Bangka Beliting, wurin da ake tsamani jirgin ya fada. Malaysiya kuma ta tura jiragen ruwan yaki 3 da jirgin sama 1, yayin da Singapore kuwa ta tura wani jirgin saman sufuri samfurin C-130 zuwa wurin.
Har wa yau, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta nuna a ran 29 ga wata cewa, Sin ita ma tana shirin tura jiragen sama da jiragen ruwanta zuwa wurin domin neman wannan jirgin da taimakawa wajen gudanar da aikin ceto, tare da ba da taimako idan har kasar Indonesiya take da bukata.
Sojojin Indonesiya sun nuna cewa, ba a samu wani ci gaba ba har yanzu, kuma har yanzu ba a hakikance faduwar jirgin ba ko kuma ya sauka wani wurin da ba a san shi ba.
Kuma gidan telibijin na Metro na kasar Indonesiya ya ruwaito maganar jami'in yanayin sama na cewa a lokacin da jirgin ya bace, ana fuskantar yanayin sama mai tsanani a sararin tekun, amma bai bayyana ko akwai alaka tsakanin hadari da yanayin sama ba. (Amina)