in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jirgin sojan Najeriya ya fadi a Bama na jihar Borno
2014-07-22 09:32:57 cri

Hukumomin sojan Najeriya sun bayyana cewa, wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojan kasar ya fadi a yankin kudancin Bama da ke jihar Borno mai fama da tashin hankali da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Kakakin hukumar tsaron kasar Chris Olukolade ya bayyana cewa, jirgin mai lamba Mi-35 ya fadi ne sakamakon matsalar na'urar da ya samu a lokacin da yake a wani aikin horo a yankin na Bama da ke jihar ta Borno.

Jami'in ya ce, babu wanda ya jikkata sanadiyar hadarin, ko da yake an fara gudanar da bincike don gano musabbin hadarin. Duk da cewa sojojin na artabu da mayakan kungiyar Boko Haram a yankin, amma ba harbo jirgin aka yi ba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China