Kungiyar kamfanonin jiragen saman Afrika (AFRAA) ta ba da sanarwa a ranar Alhamis cewa, kamfanonin jiragen sama guda 40 suka cimma nasarar samun satifiket na binciken ayyukan tsaro na kungiyar sufurin jigaren saman kasa da kasa (IATA).
Sakatare janar na kungiyar AFRAA, Elijah Chingosho ya bayyana a birnin Nairobi cewa, gwamnatocin Afrika sun tsai da shekarar 2015 a matsayin shekarar karshe ga kamfanonin jiragen saman nahiyar da su cika sharuda da ka'idojin da aka sanya musu a wannan fanni, in ji mista Chingosho a yayin wani taron manema labarai kan taron kungiyar masu samar da kayayyaki da masu ruwa da tsaki game da sufurin jiragen sama karo na uku da za'a shirya a Nairobi daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Mayu. (Maman Ada)