Yan sandan filin jirgin saman Geneva sun bayyana cewa, an damke mutumin da ya yi fashin jirgin saman kasar Habasha da ke kan hanyarsa ta zuwa Rome, amma aka canja akalarsa zuwa Geneva a ranar Litinin da safe, kuma dukkan fasinjoji da ma'aikatan jirgin suna cikin koshin lafiya.
Ko da yake an rufe filin saukar jiragen saman na dan wani lokaci, amma 'yan sanda sun bayyana cewa, al'amura sun daidaita.
Shi dai wannan jirgin kirar Boeing 767-300, wanda ya tashi daga Addis Ababa na kasar Habasha a kan hanyarsa ta zuwa Milan inda zai ratsa da Rome, an tilasta masa sauka ne a filin saukar jiragen sama na kasa da kasa da ke Geneva da misalin karfe 6 na safiyar ranar Litinin, agogon wurin, bayan da aka bayar da rahoton cewa, an yi fashin sa a sararin samaniyar kasar Sudan. (Ibrahim)