Wani jirgin saman sojin kasar Aljeriya da ya fadi a wani yanki mai yawan tsaunika dake gabashin kasar ya hallaka mutane 77, tare da jikkata wani mutum daya.
Wata jaridar kasar mai suna El Watan, ta rawaito ministan tsaron kasar ta Aljeriya na cewa, tuni aka debe gawawwakin mutane 76 da suka rasa rayukansu, sai dai akwai mutum guda da ba a tantance da halin da yake ciki ba.
An kuma gano daya daga cikin akwatin na'urorin dake nadar bayanan halin da jirgin ke ciki.
Jirgin dai wanda ya tashi dauke da mutane 78 a ranar Talata 11 ga watan nan, ana alakanta faduwarsa ne da rashin kyakkyawan yanayin sararin samaniya, sakamakon kakkarfar iska da dusar kankara dake sauka a lokacin.
Jaridar ta rawaito shugaba Abdelaziz Bouteflika na bayyana sojojin da jirgin ya fadi da su a matsayin shahidai, tare da ayyana kwanaki 3 a matsayin ranekun zaman makoki a dukkanin fadin kasar daga Larabar nan.
Wannan hadari dai shi ne irin sa mafi muni da kasar Aljeriya ta fuskanta, tun bayan wani hadarin jirgin da ya yi sanadiyar rasuwar mutane 102 a shekarar 2003. (Saminu)