in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 40 sun rasu sanadiyyar faduwar jirgin saman fasinjan Iran
2014-08-10 16:53:20 cri
Bisa labarin da wasu kafofin watsa labaran kasar Iran suka yada a Lahadin nan, an ce a kalla mutane 40 ne suka rasu, sakamakon faduwar wani jirgin saman fasinjan kasar mai dauke da mutane 48.

Rahotanni sun ce jirgin wanda ya fadi a filin jirgin saman Mehrabad dake babban birnin kasar Tehran, na yunkurin barin filin ne zuwa birnin Tabas dake gabashin kasar.

An dai ce mai iyuwa ne, matsalar da wani injin jirgin ce ta haddasa hadarin.

Bugu da kari, wani gidan Talabijin mallakar kasar ta Iran ya ce jirgin saman na aiki ne bisa fasahohin sarrafa jiragen sama na kasar Ukraine. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China