Shugaba Xi ya gabatar da sakon na sa ne ya yin da yake ziyarar aiki a kasar Argentina.
A kuma jiya Asabar bangarori daban daban na ci gaba da tattaunawa game da hadarin jirgin saman na Malaysia. Ya yin da a hannu guda aka fara aikin tantance gawawwakin wadanda hadarin ya rutsa da su da kuma jigilar su zuwa kasashen su.
A zangon farko dai an debe gawawwakin fasinjoji 38, daga wurin da hadarin ya auku. Kawo yanzu kuma likitoci 50 daga jihar Donetsk suna ci gaba da aiki a wurin.
Tuni kuma tawagar kungiyar tsaro da hadin gwiwa ta nahiyar Turai ta (OSCE) ta isa wannan wuri, inda ta zanta da wasu mazauna wurin, da masu aikin ceto, da kuma likitoci domin fayyace halin da ake ciki.
A daya bangaren kuma, Firaministan Jamhuriyar jama'ar Donetsk, Alexander Borodai ya shaidawa kafofin yada labaran kasar cewa, ana cikin mawuyacin yanayi a wurin da hadarin ya auku, domin tuni wasu gawawwakin fasinjojin suka fara lalacewa, ya yin da wasu kuma suka fada gidajen mutanen dake yankin, lamarin da ya sanya tsananin bukatar kawar da su. Koda yake a hannu guda wasu kwararru na bukatar a bar gawawwakin, da tarkacen jirgin a wurin da suke, har ya zuwa lokacin da kwamitin bincike zai gudanar da aikin sa.
Bugu da kari Firaminista Borodai ya yi kira ga kwararrun da za su gudanar da bincike, da su gaggauta fara aiki domin warware matsalar da ake ciki. Ya ce, duk wani jinkiri na iya kawo karin cikas ga binciken.(Fatima)