in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jiragen ruwan Sin za su ci gaba da aikin laluben jirgin saman Malaysia da ya bace a karkashin ruwa
2014-05-03 16:25:11 cri
Yanzu ana ci gaba da aikin neman jirgin saman Malaysia da ya bace. A wani labari daga cibiyar ceto a yankin teku ta Sin cewa, an ce yanzu an canza aikin nema ta sararin sama da kan ruwa zuwa karkashin ruwa, don haka cibiyar ta kara kwarewargyara tsarin ma'aikatanta dake aikin ceto dake a wurin, kuma ta tura jiragen ruwan dake kwarewa wajenmasu fasahohin gudanar da aikin lalube a karkashin ruwa zuwa yankin da ake wannan aiki, a kokarin ci gaba da aiki bisa iyakacin kokarinsu.

Mataimakin darektan cibiyar ceto a yankin teku ta Sin, Wang Zhenliang ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, jirgin ruwan soja mai lamba 872 dake da kwarewa sosai wajen yin lalube a karkashin ruwa ya riga ya tashi zuwa kudancin tekun Indiya. An yi kiyasin cewa, zai isa wannan wuriwurin da ake aikin laluben jirgin a ranar 10 ga wata.

Haka kuma nan da 'yan kwanaki masu zuwa, Sin da Malaysia da Australia za su yi taron ministoci a Australia, domin tattauna shirin aikin lalube na dogon lokaci.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China