An mai da gawawwakin mutane 14, zuwa Maputo, daga cikin gawawwaki 16, 'yan asalin Mozambique, wadanda suka rasa rayukansu, a sakamakon wani hadarin jirgi da aka yi a watan Nawumba da ya gabata a Namibia.
Jirgin saman kasar Mozambique ya yi amanna a bisa cewar, aikin tantance gawawwakin jama'ar da suka rasa rayukansu, wani aiki ne mai wahalar gaske da kuma daukar tsawon lokaci, a inda wani jami'i na jirgin ya kara da cewar, kawo ya zuwa yanzu ana ci gaba da binciken gawawwaki guda biyu, a Namibia domin a tantance su.
A dai ranar 29 ga watan Nawumban da ya wuce ne jirgin saman TM470, wanda an shirya zai je Angola, to amma sai jirgin ya yi hadari a arewa maso gabashin Namibia, a inda a wancan lokacin ya kashe fasinjoji 27, har da wani basine a ciki, da kuma masu aikin kula da jama'a na cikin jirgin har su shida.
Bincike dai ya nuna cewar, matukin jirgin shi ne ya kayar da jirgin yana sane da gangan. (Suwaiba)