Tun lokacin da kasar Malaysia ta fitar da rahoto game da wurin da mai yiwuwa jirgin samanta kirar MH370 ya bace, ya zuwa yanzu, tawagogin aikin ceto na kasa da kasa da dama da suka hada da kasashen Sin, Malaysia, Indonesia, Vietnam, Philippines da Amurka da sauransu, sun riga sun isa wurin don dukufa wajen gudanar da aikin ceto cikin hadin gwiwa. Daga bisani kuma, kasar Japan ta bayyana cewa, za ta dukufa wajen neman jirgin sama da ya bace. A yau Talata 11 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Koriya ta Kudu Cho Teayoung ya bayyana cewa, gwamnati da jama'ar kasar suna fatan mutanen da ke cikin wannan jirgin sama za su dawo gidajensu cikin zaman lafiya. (Maryam)