in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta fara amfani da jirgin sama mai sarrafa kansa na farko
2013-12-18 12:04:56 cri

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan a ranar Talatan nan 17 ga wata ya ce, aka fara amfani da jirgin sama mai sarrafa da kansa na farko a jihar Kaduna dake arewacin kasar wadda rundunar sojin sama ta kasar ta kirkiro, ta kuma hada da kanta mai suna Gulma.

Da yake jawabin wajen kaddamar da jirgin, shugaba Jonathan ya ce, samar da wannan jirgin wani babban cigaba ne a tarihin kasar domin baya ga aiwatar da wassu ayyuka na soji, jirgin zai kuma samar da gudummuwa wajen kare aukuwar bala'u, sa ido a kan hanyoyi, samar da doka da oda, sannan kuma za'a iya amfani da shi ta hanyar zane da fitar da taswira, sadarwa da lura da yanayi.

Shugaban na Najeriya ya lura cewa, wannan jirgi mai suna Gulma zai yi matukar amfani wajen samar da labaran lura da muhalli da kuma wajen hakar albarkatun mai da gas.

Ya nuna jin dadinsa ganin cewa, rundunar sojin saman baya ga kudurinta na samar da tsaron kasa, tana kuma ba da taimako wajen ganin rundunar sojin kasar ta yi gaba a cikin tsarinta na sauran kasashe a bangaren kimiyya da fasaha, tare da ganin an tabbatar da fararen hula na taka tsantsan da bin doka.

Daga nan sai shugaban na Najeriya ya yaba wa babban hafsan hafsoshin rundunar sojin sama na kasar da rundunar sojin saman kanta bisa ga wannan nasara, ya ce, hakan zai karfafa kasar bayan inganta karfinta wajen samar da zaman lafiya da hana aukuwar tashin hankali. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China