A cewar mataimakin darektan ofishin cibiyar aikin ceto a yankin teku ta Sin, Zhuo Li, Australia ta kebe yankunan teku dake gabashi da na yammacin kasar. Inda fadin yankin yammacin gabashin ya kai kimanin murabba'in kilomita dubu 2515, yayin da na gabashi yammaci ke da fadin murabba'in kilomita dubu 1525, inda jiragen ruwan Sin za su ci gaba da aikin laluben jirgin. A nannu hannu guda suma jiragen ruwan Australia, da na Birtaniya, da na Amurka da kuma na Malaysia da sauransu na ci gaba da aikin laluben a wasu sassa.
Har ila yau shima firaministan Australia Tony Abbott ya bayyana cewa, mai yiwuwa ne a ci gaba da wannan aikin aikin tsahon lokaci.
Kafofin yada labarai na Australia sun labarta cewa, a jiya Asabar, firaministan kasar ya sake yin fashi baki kan aikin neman wannan jirgi da ake yi, yayin ziyarar da ya kawo nan kasar Sin, inda ya ce, sakwannin da aka samu daga karkashin teku, wanda ake zaton daga akwatin nadar bayanan wancan jirgi na Malaysia ne suna raguwa cikin sauri.
Kaza lika, Mr. Abbott ya nanata cewa, kasar sa ta yi imani cewa, wannan sauti na na'urar jirgin saman da ake nema ne. Amma a sa'i daya kuma ya ce, ana fuskantar matsaloli da dama wajen gudanar da aikin laluben. (Fatima)