Ya zuwa yanzu dai, yawan kasashen dake ba da tallafi wajen neman jirgin sun karu zuwa 26.
A ran 17 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana cewa, kasar Sin ta sauya shiyyar dake gudanar da aikin bincike, zuwa sauran wurare a maimakon yankunan tekun Kudancin kasar, ta kuma sha alwashin kara azamar neman jirgin yadda ya kamata.
Har wa yau a dai wannan rana ne, kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric ya bayyana cewa, a kwanan baya, kungiyar yerjejeniyar hana gwajin makaman nukiliya ta tabbatar da cewa, ba ta samun rahoton fashewa, ko faduwar jirgin saman a kasa ko a teku ba.
Da kuma karfe 8 na safiyar ranar 18 ga watan nan ne dukkan jiragen ruwan kasar ta Sin, dake jira a sashen bakin tekun kasar Thailand, suka tashi zuwa kasar Singapore, a shirin su na zuwa wasu shiyyoyi biyu dake kudu da arewaci don gudanar da aikin binciken jirgin da za a fara a nan gaba. (Maryam)