Julius Thairu, darektan shiyya na Kenya Airways reshen yammacin Afrika, Amurka, Turai da Asiya ya bayyana a ranar Jumma'a cewa bisa huldar dangantakar da aka cimma da zata fara aiki a ranar daya ga watan Satumba, jirgin saman samfurin Boeing 737 na kamfanin jiragen saman kasa zai rika zirga zirga sau uku a mako.
Wadannan sabbin tashin jirgi zasu maye gurbin tashin jirgin uku na kowa ne mako na kamfanin Delta tsakanin filin jiragen saman kasa da kasa na Robert dake Monrovia da Accra. Ta bada damar zuwa kai tsaye tsakanin Liberiya da New York da wannan hanyar zirga zirga da kamfanin Delta ya dauki nauyi, kokarin Kenya Airways na hada Afrika da sauran yakunan duniya na samun karfafuwa in ji mista Thairu a cikin wata sanarwa da aka fitar a birnin Nairobi.
Wannan zai baiwa abokan kasuwancin Afrika, karin hanya, mai kyau da inganci wajen zuwa Amurka ta kamfanin Delta Air Lines. Wani mataki ne na dabarun mu na samun bunkasuwa cikin dogon lokaci dake da manufar karfafa karfin mu a duniya in ji darekta. (Maman Ada)