in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani kamfanin Ghana ya ki amincewa ya yi laifi yayin tuka jirgin sama zuwa Iran
2014-04-21 15:19:20 cri

Wani kamfanin hakar ma'adinai, wanda aka yi wa lakabi da kamfanin injiniyoyi da masu gudanar da tsare-tsare ya ce, ko kadan bai aikata wani laifi ba a yayin da ya tuka jirgi zuwa kasar Iran, kamfanin ya yi nuni da cewar, bai karya wata doka ba ta duniya ta tukin jirgin sama, a yayin da jirgin kamfanin ya sabka a Tehran.

Wannan mai da martani ya biyo bayan wasu jawabai da aka buga a jaridar New York Times, wanda kuma daga nan kafofin watsa labarai da yawa suka yi amfani da rahoton wanda ya yi magana a game da bulaguron da jirgin saman ya yi, wanda asalinsa jirgin na Amurka ne, duk kuwa da yake cewar, Amurka ta gindaya wa kasar Iran, mai arzikin man fetur takunkumi.

Ita jaridar New York Times, wacce ta fara bayar da labarin na fara ganin jirgin a Iran, ta yi bayanai a ranar Asabar wanda suka hada da cewar, jirgin na da alaka da Ghana.

Jaridar ta ce, wasu takardun sirri na jirgin sun nuna cewar, jirgin, an ba shi amana ne a hannun bankin Utah, a madadin kamfanin na hakar ma'adinai, mai gudanar da ayyukan injiniya da tsare-tsare wanda ke da hedkwata a Accra, babban birnin Ghana. Kamfanin na Ghana yana amfani da jirgin saboda yarjejeniyar da aka kulla tsakanin bankin na Amurka da kuma kamfaninsa.

Jaridar ta kara da cewar, shugaban kamfanin hakar ma'adinan, Ibrahim Mahama, 'dan uwan ga shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama ya yi zargin cewar, an yi amfani da jirgin domin daukar kusoshin gwamnatin Ghana zuwa Tehran.

To amma babban darektan gudanarwa na kamfanin Adi Ayitevie, ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Asabar cewar, an yi amfani da jirgin ne kawai wajen daukar wani gungun 'yan kasuwar Ghana zuwa Iran. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China